1 Timothy 5

Shawara game da Gwauraye, Dattawa da kuma Bayi

1Kada ka tsauta wa dattijo, sai dai ka gargaɗe shi a matsayinka. Ka ɗauki samari a matsayin ʼyanʼuwanka, 2tsofaffin mata kuwa sai ka ce uwaye, ʼyan mata kuma a matsayin ʼyanʼuwa da matuƙar tsarki.

3Ka girmama gwauraye waɗanda suke cikin bukata ta ainihi. 4Amma in gwauruwa tana da ʼyaʼya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah. 5Gwauruwa wadda ba ta da kowa da zai taimake ta, za ta sa zuciyarta ga Allah, tana roƙo da adduʼoʼi dare da rana gare shi don taimako. 6Amma gwauruwar da take zaman jin daɗi, matacciya ce tun tana da rai. 7Ka umarce su game da waɗannan abubuwa, don su kasance marasa abin zargi. 8In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.

9Kada a lasafta gwauruwa cikin jerin gwauraye sai ta wuce shekara sittin, ta kuma yi zaman aminci ga mijinta,
Ko kuwa ta auri miji guda kawai
10aka kuma san ta sosai saboda ayyuka masu kyau, kamar renon ʼyaʼya, da karɓan baƙi, tana yi wa tsarkaka hidima, tana taimakon waɗanda suke cikin wahala tana kuma ba da kanta ga yin kowane aikin mai kyau.

11Game da gwauraye masu ƙuruciya kuwa, kada ka sa su cikin wannan lissafi. Gama saʼad da shaʼawar jikinsu ta kāsa ɗaurewa game da waʼadin da suka yi da Kiristi, sai su so yin aure. 12Ta haka suna jawo wa kansu hukunci, saboda sun karya alkawarinsu na farko. 13Ban da haka, sukan koyi zaman banza, suna zirga zirga gida gida. Ba kawai sun zama masu zaman banza ba, har ma sun zama masu gulma da masu shisshigi, suna faɗin abubuwan da bai kamata su faɗa ba. 14Saboda haka ina ba wa gwauraye masu ƙuruciya shawara su yi aure, su sami ʼyaʼya, su lura da gidajensu kada kuwa su ba abokin gāba zarafin ɓata suna. 15Waɗansu dai sun riga sun ɓaude sun bi Shaiɗan.

16In mace mai bi tana da gwauraye a iyalinta, ya kamata ta taimake su, kada ta bar wa ikkilisiya wannan nauyi, domin ikkilisiya ta sami zarafin taimakon gwaurayen da suke da bukata ta ainihi.

17Dattawan da suka bi da alʼamuran ikkilisiya da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman waɗanda aikinsu waʼazi ne da kuma koyarwa. 18Gama Nassi ya ce, “Kada ka sa wa bijimi takunkumi yayinda yake sussukar hatsi.”
M Sh 25.4
da kuma, “Maʼaikaci ya cancanci hakkinsa.”
Luk 10.7
19Kada ka saurari ƙara game da dattijo sai da shaidu biyu ko uku. 20Waɗanda suka yi zunubi kuwa a kwaɓe su a fili, don saura su ji tsoro.

21Na gama ka da Allah, da Kiristi Yesu, da kuma zaɓaɓɓun malaʼiku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ƙwarai da gaske, kada ka nuna bambanci.

22Kada ka yi garajen ɗibiya hannuwa, kada kuma ka yi tarayya a cikin zunuban waɗansu. Ka kiyaye kanka da tsarki.

23Ka daina shan ruwa kaɗai, yi amfani da ruwan inabi kaɗan saboda cikinka da kuma yawan rashin lafiyarka.

24Zunuban waɗansu mutane a fili suke, suna shan gabansu zuwa hukunci; zunuban waɗansu kuwa sukan bi su a baya. 25Haka ma ayyuka nagari a fili suke, ko ba ma a fili suke ba, ba a iya ɓoye su.

Copyright information for HauSRK